Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Yiwa Mawaka Kallon Biyu Ahu


Mubarak Nuhu
Mubarak Nuhu

A shirinmu na nishadi a yau mun zanta da Mubarak Nuhu Alhasan, wanda aka fi sani da MK, ne mawakin hip-hop wanda ya shafe shekaru yana waka.

MK ya ce ya fara sha’awar waka ne sakamakon yawan jin wakokinsu mawaka kamar Billy O, wanda shi ne gwarzonsa , sanadiyarsa ne ya fara waka. Ya kuma samu damar rera waka da gwarzonsa a wata waka ta ‘Sardauna bahago dan Hassan’.

Ya kuma ce ya fitar da wata wakar mai suna ‘Talatu”wakar da ya rera ba tare da ya rubuta ta ba.

Yana mai cewa wakar Talatu ita ce karon farko da ya rera waka ba tare da ya rubuta ta ba, kamar yadda akan ce yau da gobe ta wuce wasa, yana shiga studio sai baitocin suka rika zuwan masa kamar wahayi.

Sannan ya ce yana waka ne da zumar fadakarwa da kuma nishadantar da masu sauraro

MK ya ce babban kalulabensa shine yadda ake yiwa mawaki kallon dan iska sakamakon wadanda suka fara waka a da , akan alakantasu da rashin tarbiya da kuma akasari a wancan lokaci suna waka ne a gidajen bariki.

MK ya Kuma ce yana fata a gaba zai dinga sirkawa da yin wakokin da zarar basirar sun zo masa a kwakwalwa ba tare da ya rubuta su ba, burinsa duniya ta san shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG