Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Fafatawa Da Wasu 'Yan Najeriya A Cin Lambobin Yabon CAF


An zabi wasu ‘yan kwallon Najeriya, domin fafatawa a neman ci lambobin yabo, na hukumar kwallon kafa ta Afirka, da hadin giuwar kamfanin sadarwar na Glo.Wadanda aka zaba sun hada Alex Iwobi, Kelechi Iheanacho da Asisat Oshoala.

Ita dai Asisat, zata fafata ne da Janine Van ta Afirka ta kudu, da Gabrrielle Onguene da Raissa Feudjlo, ‘yan kasar Kamaru, da kuma Elizabeth Addo, ta kasar Ghana, a matsayin macen da tafi iya taka leda.

Kelechi Iheanacho, wanda yake takawa Manchester City, leda, da Oghenekaro Etebo, duk ‘yan Najeriya, da Ramadan Sobhi, dan kasar Masar da kuma Elia Meschak, dan kasar Congo, zasu fafata a lambar yabo na hazikin dan wasa.

Alex Iwobi, na Najeriya, da Frank Kessie, dan kasar Cote d’Ivoire, Eric Ayiah, Ghana, sai Sidiki Maiga, daga kasar Mali, sai kuma mace ‘yar Ghana, Sandra Ansah, su kuma sun fito a rukunin matasan ‘yan wasa wanda ake sa ran cewa daya daga cikinsu ne zai lashe.

Za’a dai a gudanar da wannan bikin ne a ranar 5, ga watan Janairu, na shekara mai zuwa a birnin Abuja, na Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:19 0:00

XS
SM
MD
LG