Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Farautar Wasu 'Yan Wasan Kwallon Kafa


A bangaren cinikayyar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya wadda za'a bude a watan Janairu dubu biyu da sha takwas, 2018, Newcastle United tace tana bukata dan wasan Manchester United, Luka Shaw, amma bata son biyan fam miliyan £20 kamar yadda kulob dinsa ke nema.

Manchester United ta fara tattaunawa da dan wasan tsakiyar ta Fellaini mai shekaru 30, da haihuwa, domin yuwar sabunta kwangilarsa a kungiyar, inda zai karkare a karshen kakar wasan bana.

Real Betis da Valencia suna zawarcin dan wasan gaba na Liverpool Daniel Sturridge mai shekaru 28, a duniya, ita kuwa Crystal palace tace tana da karfin gwiwa wajen cimma yarjejeniya kan sayen mai tsaron raga na kungiyar Espanyol Diego Lopez mai shekaru 36. da haihuwa.

Real Madrid tace har yanzu bata yanke shawara kan dauko mai tsaron ragar Chelsea Thibaut Courtois, ba, sai dai ta maida han kalinta ne kan David De Gea na Manchester United da kuma mai tsaron raga na Athletic Bilbao Kepa Arrizabalaga, don ganin ta dauko daya daga cikinsu a watan Janairu nan.

Kungiyar Arsenal tace zatayi kokarinta na karshe wajan ganin dan wasan ta Mesul Ozil ya sabunta kwangilarsa a kungiyar inda Barcelona da Manchester United suka kwallafa ransu dan ganin sun dauke dan wasan mai shekaru 29, daga kungiyar sa ta Arsenal, a watan Janairu nan.

Oliver Giroud na Arsenal na bukatar barin kungiyar zuwa inda zai samu kansa a wasannin domin kasar sa ta Faransa ta sa shi cikin jerin sunayen ‘yan wasanta da zasu fafata a gasar cin kofin duniya 2018.

Barcelona tana zawarcin dan wasan gaba na AC Milan Andre Silva, Arsenal tana bukatar ganin ta dauko dan wasan tsakiya na kungiyar Udinese mai suna Jakub Jankto, Chelsea tana zawarcin dan wasan tsakiya daga CSKA Moscow mai suna Alexandar Golovin, akan kudi fam miliyan £15.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG