Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Kwamtin Amintattu na Basalona da Yinkurin Sayar da Lionel Messi


Fitaccen dan wasan gaba na Basalona Lionel Messi.
Fitaccen dan wasan gaba na Basalona Lionel Messi.

Dan takarar shugabanci Basalona Augusti Benedito yayi zargin cewa kwamitin gudanarwa na kulab din na kokarin sayar da fitaccen dan wasan ta Lionel Messi.

A halin yanzu shugaban Catalans mai ci yanzu Joseep Maria Bartomeu, ya nuna ra’ayin sa da fatan cewar danwasan gaba na Argentine zai kasance a sansanin Nou zuwa shekru da dama masu zuwa.

Sai dai Benedito cewa yayi sakonnin dake fitowa daga kwamitin gudanarwar Basa ya nuna cewar baza a iya yarda da shi ba.

A wata hira da ya yi ta musamman da mujallar Goal Benedito ya ce “bayanan da suke fitawar a baina jama’a ba dai dai yake da ainihin ra’ayinsu ba.”

Ya kara da cewa a wasu lokuta suna Magana da ta saba yadda suke aiwatar da ayyukansu, ina fata a wannan lamari na Messi ba za a samu haka ba.

##caption:Fitaccen dan wasan gaba na Basalona Lionel Messi.##

XS
SM
MD
LG