Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zabi Harry Kane A Matsayin Gwarzon Dan Wasa


An zabi dan wasan gaba na kungiyar Tottenham Harry Kane, a matsayin gwarzon dan wasan kwallon Kafa bangaren Maza na kasar Ingila na shekarar 2017.

Harry Kane, mai shekaru 24 da haihuwa ya samu gagarumin rinjaye na kashi 75% cikin kuri'u na magoya bayan kwallon Kafa na kasar Ingila da suka kada kuri'un su. Dan wasan ya samu wannan nasararne sakamakon fafatawa a wasu wasannin har guda shida daban daban da ya buga wa kasarsa ta Ingila.

Bayan haka daya daga cikin abin da ya taimaka wajan samun nasarar zabensa shine dan wasan da ya jefa kwallo daya wacce ta bada dama ga kasar ta Ingila ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya 2018, shine wasansu da kasar Slovenia inda aka tashi 1-0.

kuma a yanzu shi dan wasan da ya fi kowanne dan wasan kwallon Kafa zurara kwallaye a raga na nahiyar turai inda ya jefa 56 a wasanni daban daban na shekarar 2017, dama Firimiya lig na kasar Ingila.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:56 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG