Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Dan Wasan Real Madrid Jose Antonio Reyes


Jose Antonio Reyes,

Dubban mutane ne suka halarci jana’izar tsohon dan wasan Real Madrid da Arsenal, Jose Antonio Reyes, wanda ya mutu sakamakon hatsarin mota a karshen makon da ya gabata.

An lullube akwatin gawar Reyes da tutar kungiyar da ya fara buga wasa tun yana dan yaro, aka tafi da shi har zuwa garinsu, Utrera, gabanin addu’o’in jana’iza a wata majami’ar da ke garin.

A ranar Asabar ne dan wasan mai shekara 35 da haihuwa wanda tsohon dan wasan tawagar kwallon kafa kasar Spainne ya mutu a hatsarin mota a kan hanyarsa daga Sevilla zuwa garinsu Utrera.

Hatsarn ya sa wuta ta tashi ta kuma yi sanadin mutuwarsa da wani dan kawunsa.

Sai dai akwai wani mutum guda da ke tare da su a cikin motar wanda yanzu haka yana karbar magani a asibiti saboda raunukan da ya ji kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.

An bayyana cewa dan wasan Reyes yana matsanancin gudu ne da ya kai na kilomita 200 a sa’a guda lokacin da hatsarin ya auku.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG