Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsamo Naurar Daukar Bayanai na Jirgin Airasia Daya Fada Tekun Java


Wani Bangaren Jirgin Airasia
Wani Bangaren Jirgin Airasia

Masu ninkaya na sojojin mayakan ruwa na kasar Indonesia sun tsamo naurar dake daukar bayanai kan yanayin jirgin saman nan da ya fada cikin tekun Java makonni biyu da suka wuce.
Nasarar ba karamar cigaba ba ce a kokarin gano musabbabin hadarin.
Za’a kai naurar Jakarta, babban Birnin kasar inda za’a kwashi makonni biyu ana nazari akan bayanan da ta kunsa.
‘Yan ninkayan sun kuma gano inda naurar dake daukan muryar matukin jirgin take amma basu iya fitar da ita ba domin tana karkashin baraguzan jirgin.

Gano naurorin zasu taimaka a san dalilan da suka sa jirgin ya rikito daga sama ya tsunduma cikin takun ranar 28 ga watan Disamba har ya kashe mutane 162 da yake dauke dasu.

XS
SM
MD
LG