Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Maradona A Matsayin Sabon Manajan Kungiyar Dorados De Sinaloa


Diego Maradona

An nada tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Argentina Diego Maradona, a matsayin sabon manajan kulob din Dorados de Sinaloa dake kasar Mexico.

Maradona mai shekaru 57 da haihuwa wanda ya lashe gasar cin kofin duniya wa kasarsa ta Agentina yayin da yake taka leda, ya buga wa kasarsa wasanni sau 91 tsakanin shekara ta 1977 zuwa 1994 kuma ya jagoranci tawagar kasar ta Agentina daga 2008 zuwa 2010.

Aikinsa na karshe ya kasance tare da kulob din Al-Fujairah da daular Larabawa (UAE) wanda ya ƙare a watan Afrilu. Maradona zai maye gurbin Francisco Gamez, wanda aka kora a matsayin koci a ranar Alhamis.

Dan wasan mai shekaru 26 da haihuwa Jorginho ya tabbatar da cewa ya amince ya koma Manchester City, a lokacin rani, amma ya sanya hannu a kungiyar Chelsea, saboda City ta kasa tattaunawa dan cimma yarjejeniya da kungiyarsa ta Napoli.

Dan kwallon Real Madrid, mai shekarun haihuwa 22 mai suna Dani Ceballos, ya ce da ace Zinedine Zidane yaci gaba da zama a kungiyar to da yanzu shikam baya tare da kungiyar.

Juventus tace tananan tana shirin daukan dan wasan gaba na Manchester United dan kasar faransa Faransa Anthony Martial, mai shekaru 22, a duniya a matsayin kyauta da zarar ya kammala kwantirakinsa da kulob din.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG