Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kirkiro Sabon Jirgin Ruwan Yawon Duniya Mai Amfani Da Batiri


Maxlimer
Maxlimer

Sabon jirgin ruwan da a kirkiro mai amfani da batiri wanda zai kare mutane daga halaka, zai tashi daga kasar Canada ne zuwa Ingila.

Wani sabon jirgin ruwa mai suna Maxlimer, da aka kirkira ya kammala shirinsa na tafiya yawon duniya, wanda zai tashi daga Canada zuwa Ingila.

Tafiyar dai za ta dauke shi tsawon kwanaki 35, abin ban sha’awa da jirgin shi ne, babu wani fasinja da zai bi jirgin lokacin wanna tafiyar.

Jirigin mai tsawon mita 12, zai kafa tarihi domin kuwa tafiya daga kasar Canada zuwa Ingila wata tafiya ce mai matsananciyar wuya, lura da cewa tafiya ce da take tattare da haddura, na yanayi da kuma halittun ruwa.

Wannan wani gwaji ne don ganin yadda jirgin zai iya daukar mutane ya yi wannan doguwar tafiyar da su ba tare da sun shiga cikin halaka ba.

A cewar Ashley Skett na hukumar kula da Teku na kasa da kasa, idan wanna gwajin ya tafi lafiya, shi ne zai ba da damar kirkirar babban jirgi da za a dinga jigilar mutane daga wannan nahiyar zuwa wata nahiya.

Tafiya mai tswo cikin ruwa irin wannan na tattare da abubuwan al’ajabi ga masu yin ta.

Jirgin mai amfani da batiri bai da bukatar shan mai mai yawa, wanda za a dinga sarrafa shi daga kasar ta Canada har ya kai inda ake so ya isa.

Ya zuwa yanzu dai ba a sanar da ranar da jirgin zai fara wannan yawon ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG