Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kawo Mana Yaki Kuma Muma Muna Cikin Yaki Dasu Inji Sarkin Kano


Sarkin Kano Malam Muhammadu Saanusi na biyu
Sarkin Kano Malam Muhammadu Saanusi na biyu

Mai martaba Sakin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya bukaci alumar Musulmi dasu yada addini su kuma kare Najeriya, da kuma mutincin su.

Sarkin yayi wannan kira ne a lokacin da Shugabannin kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya suka ziyarci fadar sarkin a Kano domin neman tabarruki da kuma ta’aziyya da alhinin abin daya faru a masallacin Juma’a, na gidan Sarki, a cikin watan jiya.

Sarkin ya kara da cewa, “Idan mutane suka kawo yaki yakar su akiyi sai an kaisu kasa shuru da rashin Magana akan su, ko jin tsoron su ba zai hana su yi abunda suke yi ba”.

Sarkin na Kano yace “wannan fitina bata da magani illa a yaki mutanen nan a kaisu kasa, mu nan an kawo mana yaki kuma muma muna cikin yaki dasu, kuma kamata yayi duk Musulmi su san cewa yakin nan gabadaya aka kawo mana kuma mu tamaka a hada kai da jami’an tsaro a yi yakin nan idan ba haka ba, ba za’ayi maganin wannan fitinar ba”.

Jawabin Sarkin Kano - 2'35"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

XS
SM
MD
LG