Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Karrama Wadansu Zakarun Kwallon Duniya Da Kyautar Ballon d’Or


Dan wasan kungiyar Real Madrid Croatie Luka Modric
Dan wasan kungiyar Real Madrid Croatie Luka Modric

Dan wasan kasar Croatia mai taka leda a kungiyar kwallon kafa na Real Madrid dake Spain Luka Modric, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya (Ballon d’Or.) 2018, wanda mujallar wasan kwallon kafa take bayarwa duk shekara a kasar Faransa.

A jiya ne aka yi bikin mika karramawar ga dan wasan Modric a birnin Paris, hakan ya kawo karshen mamayen lashe gwarzon dan wasan FIFA da ‘yan wasa biyu, Cristiano Ronaldo da takwaransa Lionel Messi suka shafe
shekaru 10 suna musanye a tsakanin su.

Luka Modric ya taimaka wa kasarsa Croatia a gasar cin kofin duniya inda ta kai ga wasan karshe ta kare a matsayi na biyu, haka kuma ya tallafa wa Real Madrid wajan lashe gasar zakarun Nahiyar Turai 2017/18 inda ta dauka sau uku a jere.

Cristiano Ronaldo, na kungiyar Juventus shi yazo a matsi na biyu sai
Antoine Griezmann daga Atletico Madrid a matsayi na uku cikin jerin 'yan wasan.

A bangaren matasa kuwa, dan wasan kasar Faransa da PSG Kylian Mbappe ne yayi nasarar lashe sabuwar kyautar Ballon d’Or ta gwarzon dan kwallon kafa na Duniya ajin ‘yan kasa da shekaru 21 da haihuwa.
.
A gasar cin kofin Duniya na bana 2018 da ya gudana a kasar Rasha, matashin dan wasan Mbappe wanda cikin wannan wata ne zai cika shekaru 20 a duniya shine ya lashe kyautar matashin dan wasa mafi kwazo.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG