Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu Matasa 'Yan Najeriya Da Miyagun Kwayoyi A Kamaru


An kama wasu matasa ‘yan Najeriya, masu mu’amula da miyagun kwayoyi, a sansanin ‘yan gudun hijira dake kasar Kamaru.

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, tace an kama masu laifin ne dangane da mu’amala da miyagun kwayoyi a sansanin ‘yan gudun hijira.

Darakata janar, na hukumar Sani Sidi, ne ya furta haka a yayin da yake mika masu kayayyakin abinci iri daban daban a madadin Gwamnatin tarayyar Najeriya, ga mutane fiye da dubu tamanin dake sansanin ‘yan gudun hijira a kasar Kamaru.

Hukumar ta agajin gaggawa ta gargadi matasa dake sansanin, dasu guji mu’amala da miyagun kwayoyi, su kasance masu dabiya ta gari su kuma kasance jakadodin Najeriya, na gari a kasar Kamaru.

XS
SM
MD
LG