Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar da Wata Na’ura Don Taimakawa Yara Koyon Karatu.


Yara
Yara

Wani shahararen kamfani me suna Rosetta Stone da ke samar da na’urar fasaha don koyon yaruruka a duniya, ya kaddamar da wata na’ura wadda zata taimakama yara koyon karatu.

A wani hadin gwiwa da wasu kwararru a bangaren ilimi da rubuce-rubuce, wato Literacy Specialist sun kirkiro wata dabara mai suna Lexia Learning. Shi dai wannan tsarin na Rosetta an shirya shine don bama yara yan shekaru 3-7 damar iya rubutu da karatu a karon farko, wanda zasu samu ilimin na’urorin kimiyya da fasaha don fadada fahimtarsu. Ta haka ne yara zasu samu damar koyon karatu da kansu.

A cewar shugaban kamfanin Rosetta Stone Mr. Steve Swad, “Koyon karatu wata nasarar rayuwa ce” Duk ‘yaron da ya iya karatu da wuri, na da damar gama karatu batare da wata matsalaba, kuma zai samu nasara da zama wani abu a rayuwa.

Yace wannan sabuwa dabarar ta Lexia Reading core5 yanzu haka tana taimakama miliyoyin yara a nan Amurka, koyon karatu a matakin farko. Da dai wanna dabarar iyaye na samun damar koyawa yaransu karatu ta hanya mafi jin dadi da nagarta a gida.

ILIMIN YARA 1'14"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:18 0:00

Bugu da kari wannan tsarin na Lexia Learning na kunshe da manhajan karatun yara a karon farko, wanda ke dauke da kayan ilmatar wa da suka kai kimanin littatafai 600 da kuma ayyukan koyon karatu 50 kana da kuma wasannin bidiyo da ya kunshi mahiman abubuwan ilmantarwa. Wadannan abubuwa sun hada hotuna na abubuwa don yaro yasani, da yadda ake rubuta kalmomi, harma da yadda ake fadan sunayen abubuwa yadda yakamata, kai harma da karatun labarai.

XS
SM
MD
LG