Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Garkame Hojabri 'Yar Shekaru 19 A Kasar Iran


Maedeh Hojabri, matashiya mai shekaru 19 da haihuwa na da dinbin mabiya a shafinta na Instagram. Wata majiya ta bayyanawa muryar Amurka sashen Persia, cewa hukumomin kasar Iran, sun garkame ta a sakamakon wani hoton bidiyo data wallafa a shafin inda take kwasar rawa, lamarin da suka ce ya sabawa dokar kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan mata da dama na zaman gidan kaso a sakamakon wallafa hotunan su na bidiyo wanda suke taka rawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo a kasar Iran.

Wani ganau ya bayyanawa muryar Amurka sashen Persia, cewar wata guda da ya gabata ne hukumomi suka sa aka tsare matashiyar tare da wasu 'yan mata biyu da suka wallafa hotunan su a shafukan yanar gizo inda suke kwasar rawa da nishadantar da kawunan su daga cikin gida.

Hojabri, mai shekaru 19 da haihuwa 'yar asalin Tehran, na da mabiya shafinta na Instagram 6000,000, wanda ta ke wallafa hotunan ta na bidiyo inda take taka rawar wakokin kasar da na kasashen yammacin duniya daga dakint kafin a rufe mata shafin. masoyan Hojabri, sun yi ta bude wasu shafuka da sunanta suna ci gaba da rarraba hotunan ta.

Amma tun daga lokacin da aka garkame ta, har yanzu bata sake wallafa wani hoton bidiyo a shafin na ta ba. Mun sami wannan labari ne daga shafin Muryar Amurka sashen Ingilishi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG