Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Gawar Yaron Da Kada Ya Hallaka Wurin Yawon Shakatawa A Amurka


Baturen 'Yansanda a gundumar Orange,a jihar Florida dake nan Amurka, inda wurin yawon shaKatawa na zamani nan da ake kira Disneyland yake, Jerry Demings, yace an gano gawar yaron nan dan shekara biyu da haihuwa, da kada ya kama ya hallaka a daren talata.

Babban jami'in 'Yansandan ya gayawa manema labarai jiya Laraba cewa, an gano gawar yaron mai suna Lane Graves, baki dayansa a wurinda kadan ya ja yaron.

Baturen 'Yansanda yace kadan ya kashe yaron ne kawai ta wajen nitsar da shi cikin ruwa.

Yaron da uwayensa daga jihar Nebraska duk sun je Florida ne hutu.

XS
SM
MD
LG