Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Tantance 'Yan Wasa Na Rt Hon Dogara FC A Jihar Bauchi


A shirye shiryen da ake yi na fara gasar cin kofin kwallon Kafa da mai girma kakakin majalisar tarayyar Najeriya Rt Hon Yakubu Dogara, ya dauki nauyi a fadin jihar Bauchi, Karkashin jagorancin shugaban shirin wasan Alh Balarabe Douglas da Sakatare sa Mr Paul Landi, yanzu haka Matasan 'yan wasa sun fito daga sassa daban daban a fadin jihar Bauchi.

Matasa sun hallara a filin wasa na makarantar General Hassan Usman, College dake Yalwa a Jihar Bauchi, wajan tantance hazikan 'yan wasa da zasu kasance Kungiyar kwallon Kafa ta kakakin majalisar Rt Hon Yakubu Dogara (DOGARA BOYS FOOTBALL CLUB).
Ita dai wannan kungiya za'a kafa ta ne bisa umurnin kakakin majalisar tarayyar Najeriya Rt Hon Yakubu Dogara inda zai dauki nauyinsu a wannan gasa da za'ayi nan bada dadewaba wanda ya kunshi kananan hukumomi guda ashirin da suke jihar Bauchi.

Haka kuma Dogara yayi alkawarin dauko wasu masana kwallon Kafa daga cikin gida Najeriya, da kuma kasashen waje domin zakulo hazikan y'an wasa a yayin wannan gasa dan ciyar da su gaba a ta fannin kwallon Kafa a duniya.

An fara wannan atisaye na tantance 'yan wasan tun ranar Litinin 22/1/2018 za'a kammala a cikin sati guda karkarshin mai horas da 'yan wasa Coach Abdul.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG