Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Jigilar Fasinja Da Jirgi Mara Matuki (Drone) A Dubai


Kananan jirage marasa matuka da ake kira Drone a turance sun fara aikin jigilar mutane a fadin biranen kasar Dubai.

Jirgin na iya daukar mutum guda wanda nauyin sa ya kai ma’aunin kilogiram 100, wanda yake dai dai da ma’aunin (Pounds 200) kuma yana tafiyar mintuna 30 a sararin sama.

Fasinja zai zabi inda yake so jirgin ya kai shi, baya ga wannan babu abinda fasinja zai yi domin babu wani abu da matafiyin zai iya tabawa domin sarrafa wannan jirgi.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin na iya cin zangon kilomita 160, cikin awa guda, da kuma yana iya yin tashin mill 31, idan aka caza batirin sa sau guda. An fara gwajin wannan jirgi ne a shekarar 2016, a sararrin samaniyar kasar cikin nasara.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG