Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Damke Shi Yana Damfarar Mutane A Matsayin Mace Ta Yanar Gizo


Rundunar ‘yan Sandan jihar Legas, ta damke wani matashi Falope Oluwole Israel, mai shekaru ashirin da biyu, wanda ya shahara wurin damfarar mutane ta hanyar yanar gizo.

Shi dai wannan matashi, dake karatu a makarantar horar da ‘yan jarida dake Ogba, a jihar, Legas, an damke shine a wani gidan rawa dake Ikeja, alokacin da jami’an ‘yan Sandan suka bi sahun shi.

Damke wanna matashi ya biyo baya wani bikin yanar haihuwarsa da yayi a Lekki, ne inda ya kashe fiye da Naira dubu dari biyar a abinci da abin sha.

Da yake amsa tambayoyi Oluwole Isael, yace kimani shekaru biyu, kennan yake wannan harka ta damfarar mutane ta hanyar yanar gizo, inda yake yaudarar abokan huldarsa, cewa shi mace ce, ya damfari mutane fiye da talatin kafin dubun sa ta cika.

Da take tabbatar da lamarin kakakin ‘yan Sandan jihar Legas, SP Dolapo Badmos, ta gargadi jama’a, dasu kula da irin mutanen da za suyi hulda dasu a yanar gizo, domin ‘yan danfara sun bazu a duniya.

XS
SM
MD
LG