Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amitabh Bachchan Ya Doke Salman Khan Da Akshay Kumar


A wannan shekarar jarumai a Bollywood na doka gasar a shiye shiryen Talibijin inda suke gabatar da shirye shirye daban daban masu kayatarwa da nishadantarwa.

Jaruman sun hada da tsohon zuwa Amitabh Bachchan, da shirin sa Kaun Banega Crorepati 9, da Salman Khan shi kuma da shahararren shirin nan nasa na Bigg Boss, sai kuma Akshay Kumar da nashi shirin Great Laughter challenge.

A duk tsawon maku jama’a na samun shirye shirye masu kayatarwa daga wadannan jarumai, amma kuma a cikin su wanda shirinsa yafi ka karbuwa a wannan zagaye na farko da aka yi bitar shirye shiryen su shine Amitabh Bachchan.

Shirin sa ya samu karbuwa sosai a tsakanin mutane da dama wanda hakan ya daga martabar gidan Talibijin din Sony, wanda ta kafar ake watsa shirin inda ya maida shi na daya a duk fadin kasar Indiya.

Duk da kasancewar shekarun Amitabh Bachchan saba’in da biyar (75) har yanzu dan tsoho na ja a faggen fina finai da nishadantar da mutane, shi ma Salman Khan tana kai masa a shirinsa na Bigg Boss, domin kuwa shekaru uku a jere shi ke jan ragamar shirin.

Akshay Kumar wanda shi kuwa ya dan dade baya jagorantar wani shiri a Talibijin yayi kyakkyawan dawowa domin kuwa masoyansa baki har kunne domin murnar ganin sa a Talibijin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG