Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhaji Ahmad Babilon: Matsalolin Da Kananan Mawaka Ke Fuskanta


Alhaji Shitu Ahmad Babilon

A yau filin Nishadi ya samu hira da Alhaji Shitu Ahmad Babilon wanda aka fi sani da Alhaji Babilon.

Mawaki ne, marubucin waka, kuma mai shirya waka. Ya ce tilas ne ya zamana a harkar waka, komai da ruwansa, domin wani lokacin mutum ba ya samun yadda ya kamata.

Ya ce kamar kowanne mawaki, labarin sha’awa ce ta ja shi ga harka ta waka, kuma ya fara ne a shekara ta 2014 bayan ya kammala makarantarsa ta sakandare, sannan ya lura mafi yawan mawakan da suke arewa ba sa hadawa da harshen turanci.

Kasancewar shi dan arewa ne kuma mazaunin garin Jos, ya sa suka ga dacewar yin ingausa awakokin su na zamani, kuma tun da farko bai samu wata matsala ba a lokacin da ya fara waka, sai dai daga bangaren kishiyar mahaifiyarsa inda ta nuna rashin amincewarta, daga baya ta ba shi dama.

Ya ce daga cikin kalubalen da suka fuskanta dai shi ne a wasu lokutan idan aka gayyace su wasu shiri na nishadi akan tauye musu hakkin daga bangaren manyan mawaka, inda ake kin ba su dama har sai daga karshe lokacin da mutane sun gaji ko lokutan da aka fara watsewa a wuraren taron.

A wasu lokutan ma Alhaji Babilon ya kara da cewa sai aki basu hakokinsu idan sun kammala wasan su.

Saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:09:40 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG