Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alan Pardew Zai Canja Sheka Daga Newcastle


Newcastle
Newcastle

Koch din Newcastle, Alan Pardew, yana kintsa kayansa domin zuwa kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace bayan da kungiyoyin biyu suka amince akan diyyar, za’a biya.

Tun shekaran 2010, ne Pardew, ke kulla da kungiyar Newcastle, a yanzu haka shine Koch din da yafi dadewa, amma ana sa ran cewa shi zai maye gurbin Neil Warnock, na Crystal Palace.

Koda yake Crystal, na daidai, rukunin komawa mataki na baya ita kuwa Newcastle, itace ta goma aka teburin.

Kungiyar ta Crystal Palace, ce ta nemi zauranci Pardew, domin yamaye gurbin Warnock, a matsayin mai kulla da kulob din.

Ga Newcastle kuwa duk wanda aka dauka zai yi aiki ne a irin yanayin da Pardew, yayi aiki na tsuke bakin aljuhu, ba kamar yanda ake fachaka a wasu kungiyoyi ba.

Alan Pardew - 1'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:55 0:00

XS
SM
MD
LG