Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alamun Soyayyar Gaskiya -Ra'ayoyin Matasa


Masu iya Magana sun ce juma’ar da zata yi kyau tun daga labara ake gane ta, a cikin shirin samartaka na wannan makon mun sami jin ta bakin samari da ‘yan mata ne akan sahihan alamun dake nuna soyayyar gaskiya, duk da cewa jama’a da dama sun bayyana cewa abin da kamar wuya, wai gurgiwa da aure nesa.

Tambayar da muka fitar ita ce; ta yaya matashi ko matshiya zata gane masoyi ko masoyiya ta gaskiya?, akan haka ne muka sami zantawa da samari da ‘yan mata domin jin nasu ra’ayoyin maban-banta.

Idan aka tara samari goma a cewar kashi hamsin da bakwai cikin dari na ‘yan matan da suka mayar da martani akan wannan tambaya, da wuya a sami samari hudu da ke neman budurwa da zummar aure ya kawo shi, sai dai sun bayyana cewa akan dauki lokaci mai tsawo kafin soyayyar ta rikide ta zama ta gaskiya.

Ko yaya lamarin yake a bangaren samari?, ‘yan mata dai aka fi sani da tara samari a cewar wasu daga cikin samarin da suka bayyana ra’ayoyin su, dan haka duk lokacin da budurwa ta kasance mai yawan son abin daniya daga hannun saurayi ba lallai tana son sa da gaskiya ba, haka-zalika baya ga yawan bukatar abin hannu, lafazin baki da yawan kin daga waya na daga cikin alamun rashin so.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG