Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Yuwar Canjin 'Yan Wasa Tsakanin Arsenal Da Manchester City


A cigaba da hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya da akeyi kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta amince zata sayar da danwasanta mai buga mata bayan Alex Sandros, ga kungiyar Chelsea akan kudi fam miliyan £61.

Arsenal da Manchester City suna duba yuwar musanyan ‘yan wasansu Alexis Sanchez da Sergio Aguero a wannan bazarar.

Manchester United tana daf da sayen dan wasan tsakiya na Chelsea Nemanja Matic mai shekaru 28 akarshin sati, har ila yau Manchester United na shirin sayen dan wasa maisuna Radja Nainggolan daga kungiyar kwallon kafa ta Roma.

Renato Sanches na kungiyar Bayern Munich ya nesanta kansa da rade radin da akeyi na cewar zai Koma kungiyar Manchester United, danwasan yace yana nan a Bayern Munich.

Itama kungiyar AC Millan ta karyata rade radin da yake cewa Real Madrid da Manchester United na zawarcin mai tsaron ragarta Donnaruma.

Arsenal na zawarcin dan wasan gaba na kungiyar Manchester United mai suna Antony Martial, inda ita kuwa Real Madrid tana daf da sayen Mbappe mai shekaru 18 da haihuwa daga kungiyar Monaco.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:02 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG