Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Rufin Asiri a Sana'o'in Kitso Da Kunshi: Amina Muhammad


Wata mai kitso tana kan aikinta
Wata mai kitso tana kan aikinta

Amina Muhammad, mai sana’ar kitso da kunshi ta ce ta shafe shekaru takwas tana sana’ar kitso tana mai cewa tun da farko sha’awace ja hankalinta kan sana'ar.

Ta kara da cewa sana'ar akwai rufin asiri domin tana ba ta damar biyan wasu bukatunta na yau da kullum.

Amina ta ce tana sana’ar ta ta ne a gida, kuma bayan da ta kammala karatunta na sakandare.

Ta ce a wasu lokutan idan da bukatar ta bi mutum gida domin yi masa kitso ko kunshi tana zuwa, sannan daga karshe ta ce babban burinta shi ne ta taimakawa mabukata.

Ta kara da cewa tana da ra’ayin komawa makarantar gaba da sakandare domin ci gaba da karatu inda ta ce tana da muradin karatu a fannin kimiya da fasaha ko kuma fannin likitanci domin ta taimakawa mata a harkar lafiya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG