Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Gwagwarmaya Tsakanin Fina Finan Fitattun Jarumai Hudu A Bollywood


 Aamir Khan, Katrina Kaif da Abhishek Bachchan
Aamir Khan, Katrina Kaif da Abhishek Bachchan

Akwai gwagwarmaya a Bollywood ganin irin fina finan da zasu yi gogaiya da juna kamar su Raees da Kaabil, a daya bangaren kuma Shah Rukh Khan ya sami tabbacin ranar da sabon fim dinsa wanda jama’a suka dade suna dako watau gangster drama zai fito.

Akwai kuma fim din soyayya na Hrithik Roshan, na wani makaho da masoyiyarsa duk wadannan fina finai sun samarda kudade masu dim bin yawa amma batun bai tsaya anan ba .

A bana lallai akwai gwagwarmayar da zai shiga tarihi inda fina finai na jarumai daban daban zasu fito a rana daya abinda zai jawo kiki-kaka, ko wani fim zai yi rinjaya abin sai mun gani.

Babu shakka wasu fina finai zasu fito a rana daya wanda hakkan zai jawo gwagwarmaya tsakanin su, amma babu wani ko irin haka ya taba faruwa a Bollywood inda fina finan fitattun jarumai har hudu su fito a rana daya.

Irin wannan abun inda fina finai har hudu zasu fito a rana day aba zaiwa Bollywood da masana’antar fina finai alfanu ba.

Fim din Jagga Jasoos, zai ja dim bin jama’a, tunda jarumai kamar Ranbir Kapoor da Katrina Kaif, sdun dawo faggen fina finai zasu kuma fito a cikin fim din abinda jama’a suka dade suna son gani wanda kuma har da yara suma ba a barsun a baya ba tunda ba manya kadai bane suke kaunar jaruman.

Fina finan wadanda zasu yi gogaiya da juna sun hada da Shah Rukh Khan, Akshay Kumar da Aamir Khan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

XS
SM
MD
LG