Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Alaka Tsakanin Mutun Da Aljan : Haruna Mua'zu


Haruna Mua'zu Kannywood
Haruna Mua'zu Kannywood

A yau DandalinVOA ya samu bakunci fabon mai daukar nauyin shirya fina-finai Haruna Mu’azu , sabon, malamin Turanci da da harkar rubuce-rubuce wanda ya ce sha’awa ce ta sa ya fara harkar fim, inda ya fara da fim dinsa na farko wanda ya yi duba kan alakar mutum da aljan.

Ya ce babban dalilin da ya sa ya dauke wannan fagge shi ne domin nusar da al’umma cewar lailai akwai alaka tsakanin mutum da aljan muddin mutane basu rike adu’a ba.

Ya kara da cewa fim din na nuna illar wulakanta tare da kaskantar da mutum , tare da amfanin hakuri da adua a al’amuran yau da kullum.

Haruna Mua'zu, ya ce fim din dai ya waiwayi illar nan ta mata masu tsananin kishin shallake hankali da batan basira da matan yanzu kan aikita gudun fadawa ramuwar gayya ga ire-iren wadannan mata.

Ya ce fim din na cike da darussa da jan hankalin mata da cewar ire-iren wadannan matsaloli na aljan na iya faruwa ba sace fade ba ne da yan yanzu kan dauka.

Ya kara da cewa wannnan dai shine fin dinsa na farko yana kuma sa ran shirya wasu fina-finai masu alaka da matsalolin da ake fuskanta a wannan zamanin da muke ciki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:10 0:00

XS
SM
MD
LG