Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akshay Kumar Na Kan Ganiyarsa A Bollywood - In Ji Hrithik Roshan


 Akshay Kumar
Akshay Kumar

Lallai Akshay Kumar na kan ganiyarsa a fagen fina finai a Bollywood, in ji Hrithik Roshan, ya bayyana haka ne bayan da ya kalli somin tabin fim din LLB 2. Yana mai cewa duk wanda ya kalli fim din zai yadda cewa an nuna bajinta wajan shirya fim din.

Shi dai wannan fim din an hada shine a cikin kwanaki 33, kuma Shubhash Kapoor, ne darektan fim din kuma fim din ya kasance tamkar matashiya ga fim din Courtroom drama, me fari jini na shekarar 2013.

Fim din dai zai fito ranar juma’a 10, ga watan nan da muke ciki da jarumai kamar su Huma Qureshi, Saurabh Shukla da Annu Kapoor.

A shafinsa na tweeter Roshan ya rubuta cewa Akshay Kumar na ganiyarsa , “ina jinjinawa mutanen da suka hada wannan fim din a cikin kwanaki 33, da kuma yi masu barka da aiki.”

Kashin farko na wannan fim din ba kawai ya taka rawar gani bane harma da samun kyauta ta lambar yabo a kasar, kasancewar irin gagarumi aikin da aka yi a fim din na farko, Amma a yanzu jama’a suna zullumi da harsashen abinda zai kasance a wannan fim din zai fiye na farko ban mamaki da kayatarwa.

Ganin yadda har yanzu fina din Kaabil na Hrithik Roshan da Raees, na Shah Rukh Khan ke cin karensu babu babbaka a Bollywood, ana harsashen cewa LLB 2, na iya kwace kasuwar da wadannan fina finai ke murewa a halin yanzu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

XS
SM
MD
LG