Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikata Laifi A Kokarin Kaucewa Laifi

In this court room sketch, Judge Col. Tara Osborn, top, Maj. Nidal Malik Hasan, right, and defense attorney, Lt. Col. Kris Poppe, left, are shown, Wednesday, Aug. 21, 2013, in Fort Hood, Texas. Hasan rested his case Wednesday without calling any witnesses

An zargi wani matashi da laifin satar motar abokinsa, wanda yayi hakane domin kaucewa laifin rashin bayana a gaban kuliya a dalilin tuhumar sa da ake da laifin da ya danganci miyagun kwayoyi.

Matashin ‘dan shekaru ashirin da ‘daya mai suna Jorge Ramirez-Sierra, ana tuhumarsa da laifin yin amfani da kayan da bana nashi ba, da kuma yin tuki bayan an dakatar da lasin ‘din tukin sa, da sauran wasu laifuka.

‘Yan sanda sun gayawa mujallar NJ.com ta yanar gizo, cewa sabbin caje cajen sun kuno kai ne, a lokacin da wani mutum ya sanar musu cewa motar sa ta ‘bace ranar Juma’a. yakuma gayawa jami’an tsaron cewa ya ji abokinsa Ramirez-Sierra, yana fadin cewa bai san ta yadda zai je kotu a garin Paterson ba, domin sauraron karar da aka yi.

A lokacin da jami’an ‘yan sanda ke magana da mai motar sai Ramirez-Sierra ya kira ya ce yana kan haryar sa ta mayar da motar. Dawowarsa keda wuya da motar ‘yan sanda suka cafke shi.

XS
SM
MD
LG