Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFCON: Ivory Coast Ta Yi Waje Da Mali


Wasan gasar cin kofin nahiyar Afirka

Yanzu Ivory Coast ta samu damar shiga zagayen gab da na kusa da na karshe inda za ta hadu da kasar Algeria a ranar Alhamis.

Tawagar ‘yan wasan kasar Ivory Coast ta fitar da takwarorinta na Mali daga gasar cin nahiyar Afirka da ake yi a Masar.

Ivory Coast ta samu nasara ne akan Mali da ci daya mai ban haushi, bayan da dan wasanta Wilfried Zaha ya zura kwallon a minti na 76.

Yanzu ta samu damar shiga zagayen gab da na kusa da na karshe inda za ta hadu da kasar Algeria a ranar Alhamis.

An jima kadan za a kara tsakanin Ghana da Tunisia, duk wanda ya samu nasara, zai hadu da Madagascar a ranar Alhamis.

Madagascar ta fidda DR Congo daga gasar a jiya Lahadi bayan da aka yi bugun fenarti.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG