Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ademola Lookman Ya Ce Ya Gwammace Takawa Najeriya Leda


Matashin, dan wasan gaban Everton Ademola Lookman na shirin barin bugawa tawagar ‘yan wasan kasar Ingila ‘yan kasa da shekaru 21 domin dawowa Najeriya da taka leda.

Dan wasan Burtaniya ya wakilci Ƙasar Ingila tun daga under 19, U20 da matasa 21, ya kuma taimaka masu a gasar cin kofin duniya ta FIFA U20 a 2017 ta hanyar zura kwallaye uku a wasan.

Lookman ya cancanci buga wasa a tawagar Super Eagles, a kasancewar iyayensa ‘yan asalin Najeriya, amma an haife shi a Wandsworth, Ingila.

Dan wasan mai shekaru 20 da haihuwa wanda ya shafe kakar wasa ta karshe a amatsayin aro a Bundesliga, RB Leipzig, daga kungiyar Everton ya yanke shawarar canza sheka zuwa Najeriya.

Ademola ya fahimci cewa ya kamata ya takawa Najeriya wasa a farkon shekarar 2018 bayan wata ganawa da sukayi da shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG