Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aamir Khan Da Fatima Sana Shaikh Zasu Kara Nuna Bajinta A Sabon Fim


 Aamir Khan
Aamir Khan

Aamir Khan da Fatima Sana Shaikh, wadanda duk suka fito a fim din Dangal na Aamir Khan, zasu sake hadewa a wani fim mai suna Rakesh Sharma.

Dama can tun farko sunyi hadaka a fim din Yash Raj, mai suna “Thugs of Hindostan” gashi kuma yanzu akwai rade raden cewa zasu sake burgewa tare a fim din Rakesh Sharma.

Wata majiya kusa da jarumi Aamir Khan, tace jarumin ya yake shawarar sa Fatima Sana ne domin basirar ta kuma dama shine ya sharwarcin Aditya Chopra, da ya gyaiyato Fatima domin itama ta taka irin nata rawar a fim din Thugs of Hindostan.

A cikin wanna sabon fim din da zasu yi tare Fatima zata kasance matar Aamir ne a cikin sa kuma a yanzu haka ya bukace ta da ta bar sumar ta da ya toho baya da suka kamala fim din Thugs, kuma zata fara shirye shiryen turkarar matsayinta a cikin fim din.

Kasancewa Fatima ta fito a matsayin ‘yarsa a wasu fina finai a baya amma fitowarta a matsayin matarsa a wanna fim din zai nuna irin kwarewar da Aamir Khan ke dashi a faggen fina finai mai nuna cewa yana iya taka kowace irin rawa ake bukatarsa da ya taka a faggen fina finai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG