Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karo Na Goma Ronaldo Ya Zama Zakaran Kwallon Potugal


Cristiano Ronaldo

A yau talata, Fitaccen dan wasan Juventus, Cristiano Ronald, ya lashe lambar yabo ta gwarzon dan kwallon Portugal ta shekara-shekara a karo na 10.

Dan wasan mai shekaru 34 ya doke Joao Felix na kungiyar Atletico Madrid da Bernardo Silva na Manchester City don lashe kyautar.

Da yake jawabi bayan ya lashe kyautar a filin Carlos Lopes Pavilion dake Lisbon, Ronaldo ya ce: "duniyar tana kara burunkasa, tare da kafofin sadarwa da 'yan jaridu.”

Ya ce "wannan shekarar ta kasance mai matukar wahala a waje na. Kada ku bari wani wani ya karya muku gwiwa.”

Ronaldo yana cikin jerin 'yan wasa uku da hukumar kwallon kafa ta FIFA ta zaba, wadanda za’a bawa kyautar gwarzon dan wasa na maza ta duniya.

Tsohon tauraron dan wasan Real Madrid ya rasa kyautar gwarzon dan wasan kwallon Turai ta shekara-shekara wato UEFA, ga dan wasan kungiyar Liverpool, Virgil van Dijk a makon daya gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG