Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwallon Mutun-Mutumi Ta Yawace Duniyar Wata


Kwallon Mutun-mutumi
Kwallon Mutun-mutumi

Hukumar binciken sararrin samaniya ta kasar Japan, sun samu nasarar aika mutun-mutumi duniyar wata a karon farko. Tun bayan isar na'urar a karon farko na’urar ta dauko hotuna da bidiyon duniyar watan. Bayan aika na’urar da sukayi a farkon watan Yuli.

Naurar mutun-mutumin da ake sarrafa ta a wannan duniya, ta samu damar dauko hotuna, wanda suka bada masaniyar yanayin duniyar. A lokacin da masana ke fadada binciken su a duniya, na’urar ta dauke su hotuna.

Na’urar mai suna ‘International Ball Camera’ a turance, ta bayyanar da irin dama da za’a iya samu wajen gudanar da rayuwa a duniya. A cewar mahukunta na hukumar ‘Japan Aerospace Exploration Agency’ ya zuwa yanzu an fitar da hotunan farko da na’urar ta daukko a duniyar wata.

Na’urar na iya yawo zuwa kowace kusurwa a duniyar wata, batare da wani tsaiko ba, a cewar mahukuntan, dama babban makasudin aika na’urar shine ta dauko hotuna da bidiyon yanayin duniyar ta wata, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu zuwa yanzu.

Za kuma a iya amfani da na’urar wajen aiko da sakonnin gaggawa zuwa wannan duniya kai tsaye, haka ana iya ganin halin da ma’ikatan sama jannati suke ciki a yayin da suke gudanar da aikin su a duniyar watan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG