Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalubalen Bai Wuce Kin Biyan Mawaki Hakkin Sa Ba : Lamir Hassan


Lamir Hassan
Lamir Hassan

Lamir Hassan matashi mai wakar soyayyar rauji, hip hop film writer mai hada fina finan Hausa da sauransu, ya ce sha’awa ce ta ja hankalinsa da son zama mai dogaro da kai, kuma a cewarsa ya fara ne daga hada kida kana daga bisani ya fara rubuta waka.

Bayan haka ne matashin ya lura da cewar a yayin da yake rubutawa wakarsa yana samun basira da dabarun rubuta labarai wadanda a cewarsa yake juya su har daga karshe su zama labaran fim.

Lamirun Zamani yace babban abin da ke ci masa tuwo a kwarya bai wuce yadda idan ya rera waka bayan kashe kudinsa sai biyansa hakkokinsa ya zama jidali ba.

Hazikin matashin ya kara da cewa a yanzu dai ya rubuta labaran fina-finai da dama amma tsoron da yake sai ya kai labarai sai a sauya wato a fitar da fim din bayan an gama kashe masa gwiwa, inda ya ce, hakan ya faru da dama ga wasu abokansa.

Daga karshe a zantawarsu da wakiliyar dandalinvoa, ya tabbatar da yin dacen adalin da zai karbi rubutattun fina-finansu kafin ya fara saye.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG