Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daya Daga Cikin Tsegunguman Da Ke Yawo A Shafukan Sada Zumunta Na Yanar Gizo


Sananniyar ‘yar jarida wadda ta sami horo daga kasar Amurka Olunloyo, ta jawo cece-kuce da jayayya a shafukan sadarwa na yanar gizo bayan ta kafe hoton wani matashi mai shekaru 21 da haihuwa wanda ta ce shi ne take kyautata zaton zata aura.

Matar mai shekaru 52, da haihuwa ta kafe hoton masoyin nata ne me suna Hakeem, a shafinta na facebook inda ta yi masa lakabi da daya tilo a zuciyarta, da sauran kalamai makamantansu na nuna so na nuna so da kauna.

Ta kara da cewa abin kaunar nata bai cika zama wuri guda ba sakamakon yanayin aikinsa, dana haka ana iya binsa a shafinsa na yanar gizo, amma fa duk wanda ya nemi ya ci zarafinta ta akan yanar gizo, bazai ji da dadi ba daga wurin masoyin nata.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG