Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kambin Ballon d'Or Ronaldo Ko Messi


Shahararen dan wasan kwallon kafa mai taka leda a kungiyar Barcelona, Neymar, yace abokin wasansa kuma dan kungiyarsu Lionel Messi,shi zai lashe kambin fitatcen dan wasan da ya fi kowa taka leda watau Ballon d’Or na bana kambin da ake badawa a kasar Faransa.

Koda yake jama’a da dama sun raja’a akan Ronaldo, a matsayin wanda ake ganin cewa zai lashe wannan kambin na bana bayan da ya taimakawa Real Madrid, ta lashe gasar zakaru, a kakar da ta gabata.

Ronaldo, mai shekaru talatin da daya (31), yayi rawar gani a nasarar da Portugal, ta samu na lashe gasar (Euro 2016), kuma ya jefa jimilar kwallaye 51, a wasanin da ya bugawa Real Madrid.

Neymar, a nasa bangaren ya dage cewa Messi, yakamaci wannan kambin ganin cewa ya jefawa Barcelona, kwallaye 20, inda 9, daga ciki a gasar La Liga, ya jefa.

Shi kuwa Ronaldo, kwallaye 10, ya jefa a gasar ta La Liga, kuma Real Madrid ke kan saman teburin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00

XS
SM
MD
LG