Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Yanka Mai Okada Saboda Naira 50


An cafke wani matashi Abdulraham Muhammad, mai shekaru ashirin, cafke shi da rudunar ‘yan Sandan jihar Ogun, tayi ya biyo bayan yanka wani mai haya da mashin wadanda akafi sani da masu Okada, da Abdulrahaman, yayi.

Mai Okada din mai suna Owechu, da Abdulraham, sun sami wata ‘yar takaddama ne akan canjin Naira 50. A labarin da jaridar Punch, ta wallafa na nuni da cewa mai Okadan ya dauki Abdulrahaman, ne daga Ijaba zuwa Iyana Iyesi, bayan da ya kashe shi sai kuma ya gudu da mashin dinsa.

Wani mazaunin yanki yace masu Okada, a yankin sun tsayarda Abdulrahaman, bayan da suka ga jini a jikinsa sai yace yayi hadari ne yana kuma kan hanyaqrsa na zuwa asibiti ne.

Daga bisani da aka ga gawar Owechu, sai wani yaro yace tare ya gansu da Abudulrahaman Muhammad.

Labarin Mutuwar Owechu, ya dan so ya jawo hatsaniya a yankin amma da taimakon shuwagabanin al’uma da ‘yan Sanda, abin sai ya lafa.

DPO, din yankin Muyideen Obe, wanda ya tabbatar da labara yace da zarar an kammala bincike za’a gurfanar da Abdulrahamn Muhammad, a gaba kuliya.

XS
SM
MD
LG