Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin BlackBerry Zai Daina Kera Waya


A yau laraba kamfanin kera wayar hannu ta BlackBerry, ya bayyana cewa zai zai daina ci gaba da kera wayar hannu waddan ta sami karbuwa a wasu shekaru da suka gabata.

Kamfanin mai mazauni a birnin Ontario dake kasar Canada, ya bayyana cewa yana fuskantar karamcin samun kayan kera wayar ga abokin kamfanin dake kasar Indonesia, inda ya ce a maimakon haka zai mayar da hankali wajan kera manhajar na’ura mai kwakwalwa.

Yanzu haka dai kamfanin ya ce wayar BlackBerry-9720 zata fito da sunan kamfanin PT da suna Tiphone Mobile TBK dake kasar Indonesia.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG