Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Ya Yi Kisa Saboda Budurwa


Wani matashi dan shekaru ashirin da biyar da haihuwa(25), Mathew Iyede, ya gamu da ajalinsa biyo bayan wata rashin jituwa da ta shiga tsakanin sa da wani mai suna Ese Uku, akan budurwa.

Lamarin ya faru ne a wata mashaya dake kusa da jami’ar jihar Delta, Abraka, shi dai Mathew, yam utu anan take ne.

Shi dai Ese, wanda ya aikata wannan mummunar aikin da shi da wasu abokansa,Kevwe Edward, da shekaru ashirin da daya(21) da Lucky Grant dan shekaru goma sha tara,(19) ne suka yiwa Mathew, kwantan bauna a cewar jaridar Punch.

Tun farko dai Ese, ya jawa Mathew, kunnen akan cewa ya rabu da wannan yarinya domin shima ya na son ta.

An dai soki Mathew, sau da dama ne a kirjinsa, wanda ake kyautata zaton cewa shine sanadin mutuwarsa.

Da take tabbatar da labarin kakakin ‘yan Sandan jihar Delta SP, Celestina Kalu, ta ce tuni aka cafke abokan Ese Uku, su biyu a game da lamarin.

XS
SM
MD
LG