Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kafar Sada Zumunta Ta Twitter Ta Rufe Shafuka 235,000 A Dalilin Yada Ta'addanci


Kafar sada zumunci ta twitter ta fitar da sanarwar cewa ta sake rufe wasu ‘karin shafuka har 235,000 a dalilin yada akidar ta’addanci da suke, cikin watanni Shida da suka gabata.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar jiya Alhamis, yace “Wannan ya hada jimlar shafukan da muka dakatar zuwa 360,000 tun tsakiyar shekarar 2015.”

Twitter tace yawan rufe shafukan mutanen da suke yin amfani da kafar kullum, ya ‘karu da kaso 80 cikin 100 tun shekarar da ta

gabata ta 2015. Ta kuma ‘kara da cewa yawancin shafukan da aka rufe sun biyo bayan hare haren ta’addanci.

Kamfanin na Amurka, yace yanzu haka yana samun nasara wajen kare duk wadanda aka rufe shafinsu da su sake bude wani shafin ta hanyar yin amfani da wani suna na dabam, haka kuma suna aiki da sauran kafofin sadarwa wajen gano duk wani abu mai alaka da ayyukan ta’addanci.

Sai dai kuma duk da wannan ci gaba da ake samu, yawancin mutanen da aka rufewa shafinsu na samun hanyar komawa su bude wani shafin.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG