Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matashi Zai Kwashe Shekaru Tara A Gidan Wakafi Dalilin Fyade


Wata kotu a legas, ta daure wani matashi dan shekaru ashirin da tara da haihuwa mai suna Sheriff Oyewole, shekaru tara a gidan yakafi.

Hakan ya biyo bayan samun shi da laifin cin zarafin wata ‘yar shekaru ashirin da ukku da haihuwa da suka hada da bugarwa, yimata fyade da kuma daukar hoton tsaraicinta da yi mata barazanar cewa idan har ta fadawa wani abinda ya faru zai wallafa hotunan a yanar gizo.

Dan Sanda, mai gabatar da kara sufeton Nurudeen Thomas, ya fadawa kotu cewa mai laifin ya aikata wannan aika aika ne a ranar 16, ga watan Agustan shekara da ta gabata a Aro Otel dake Legas.

Ya kara da cewa haka ya sabawa sashe na !44, 171, 220, 241, 258, 261, 263, 316, da kuma 337 na kundin laifuffukan jihar Legas.

A lokacin da ya rakata zuwa wurin mahaifiyarta ne aka fuskanci cewar akwai wani data bude baki ta gaiwa mahaifiyarta abinda ya faru sai ya nemi ya ranta ana kare amma aka cafke shi aka mikawa ‘yan Sanda.

XS
SM
MD
LG