Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Argentina Na Iya Shawo Kan Messi Kuwa ?


Dan wasa Lionel Messi

Tana iya yuwa Lionel Messi, zai dawo ya ci gaba da dokawa kasar sa watau Argentina wasan kwallon kafa hakan nada nasaba ne da ganawar da suka yi da sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Argentina, Edgardo, wanda suka yi a kasar Spain inda suka dauki tsawon awa daya suna tattaunawa.

Sai dai har yanzu basu fayyace dalilin sakamakon ganawarsu ba, idan ba’a manta ba Lionel Messi da Mastherano, sun furta cewa sun sagale takalmansu na bugawa kasar su ta Argentina wasa ne baya kasar Chile da doke kasar ta Argentina a gasar “Copa America”.

Sai dai tsohon dan wasan Argentina Maradona yana ganin cewa sabon mai horara da ‘yan wasan ba zai iya shawo kan ‘yan wasan da su dawo su bugawa kasar wasa ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:07 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG