Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shahararrun 'Yan Wasa Zasu Hallara A Brazil


Ranar juma’a, 5, ga watan Agusta, ake sa ran za’a fara gasar motsa jiki na Olympic, na shekarar 2016.

Shi dai wannan gasa za’a yi shine a Rio De Janeiro dake kasar Brazil, kuma za’a kammala wasannin ne ranar 21, ga wannan watan.

Ana sa ran cewa kasashe 207, ne zasu fafata a wasanin 306, a cikin wasani 28, irin daban daban cikin wasannin har da kwallon kafa na maza dana mata.

Manyan ‘yan wasa da zasu haska a wasanin sun hada da dan wasan kasar Brazil Neymar, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da Mikel Obi, dan Najeriya, mai taka leda a kungiyar Chelsea.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:54 0:00

XS
SM
MD
LG