Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mourinho Yace Zai Yi Kokarin Yin Abinda Alex Ferguson Yayi


Jose Mourinho
Jose Mourinho

Sabon Koch din Manchester United Jose Mourinho, yace zai yi kokarin yin abinda tsohon Koch din Manchester United, sir Alex Ferguson, yayi na irin nasarorin da ya samu, da lashe gasar zakaru har sau biyu.

Tsohon mai kula da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ya furta haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai yau a karon farko tunda ya zama Koch din Manchester United.

Dan shekaru 53, wanda ya taba rike kungiyoyin kwallon kafar Chelsea, Real Madrid, Inter Milan da Porto, yace tsohon dan wasan United kuma mataimakin Koch Ryan Giggs, ya bar kungiyar ne sabili da bai samu yadda yake so ba.

XS
SM
MD
LG