Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Obi Mikel Yace Zai Bar Chelsea, Sai Fa Idan...


John Obi Mikel yana murza kwallo
John Obi Mikel yana murza kwallo

Da alamun John Obi Mikel zai iya shura takalmansa ya bar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea domin neman kungiyar da zata rika sanya shi wasa kai tsaye.

Dan wasan na tsakiya, wanda tun shekarar 2006 yake tare da Chelsea, yana da sauran shekara daya a kwantarakinsa, kuma har yanzu ba a ba shi tabbaci a kan yawan mintocin da zai rika buga wasa ma kungiyar a sabuwar kakar kwallo mai zuwa ba.

Shafin GOAL.COM ya ruwaito cewa Mikel ya tattauna da sabon manajan Chelsea, Antonio Conte, kuma yayi niyyar dakatar da barin kulob din har sai ya sake tattaunawa da sabon manajan wanda a yanzu haka shine yake jagorancin kasar Italiya a gasar cin Kofin Kasashen Turai.

Shafin yace Mikel yana kwadayin zama a Chelsea, amma kuma yana nazarin matakan da zai iya dauka idan har Conte bai fada masa abinda yake so ya ji ba.

Kungiyar Chelsea tana da wani tsari na bayar da kwantarakin shekara daya kawai ga 'yan wasan da suka haura shekara 30 da haihuwa. Wannan yana nufin cewa, zai fi kyau ma Mikel mai shekaru 29 da haihuwa a yanzu, ya sabunta kwantarakinsa a wannan shekarar domin tabbatar da cewa ya samu na dogon lokaci.

A bayan cikin watan Maris, a bayan karawar Najeriya da Masar, Mikel ya bayyana a fili cewa shi kam ya gaji da zama a kan benci in ana wasa.

Mikel ya fadawa shafin na GOAL.COM cewa "Ni dai ina son na rika bugawa a lokacin wasa a saboda abu guda da ba na so shine zama a benci kamar yadda nayi a baya. Ko ma a ina ne, ni dai ina son a rika sanya ni a wasa..."

XS
SM
MD
LG