Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kori Dan Wasa Daga Fili Bayan Da Yayi Tusa Da Karfi


Alkalin wasa ya kori wani dan wasan kwallon kafa daga fili a kasar Sweden, a bayan da ya ji wannan dan wasan ya sake tusa da karfi a lokacin wata karawa a wasannin lig-lig na kananan kulob na kasar.

Wata jaridar kasar Sweden mai suna "Aftonbladet" ta ce alkalin wasa ya ciro jan kati ya nunawa Adam Lindin Ljungkvist, ya kore shi daga wasan bisa hujjar cewa "ya aikata abinda bai kamaci dan wasa ba a cikin fili."

Shi dai Ljungkvist yana buga ma wata kungiya ce mai suna Pershagen SK, a lokacin da suke karawa da kungiyar Järna SK.

Daga bisani, dan wasabn mai shekaru 25 da haihuwa ya ce, "nayi matukar mamakin wannan jan kati da aka ba ni. Ciki na ya rude, yana damu na, kuma ana kusa da karshen wasan da muke bugawa, sai na yi tusa. Sai alkalin wasa ya ba ni Kati mai ruwan dorawa (yellow card). Daga nan sai ya ciro jan kati ya ba ni, aka kore ni daga fili a saboda wannan shine kati mai ruwan dorawa na biyu da ake ba ni. Na fusata sosai da abinda alkalin wasan yayi..."

Ljungkvist ya ci gaba da cewa "Ina tsammanin ya dauka cewa na yi tusar a jikin wani dan wasa ne, amma ai da mamaki a ce zaka tsokani dan wasan daya kungiyar da kuke karawa da su ta hanyar tusa. Ni dai kawai tusa ta kama ni ne, na sake ta, aka kuma kore ni a dalilin haka.

A karshe dai kungiyar Pershagen SK ta sha kashi a wasan da ci 5-2.

Dan wasan ya karasa da cewa "Ban taba jin wani dan wasan da aka kore shi daga filin wasa a saboda wai yayi tusa ba."

XS
SM
MD
LG