Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada-hadar Cinikayya Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Kungiyar kwallon kafa ta Leister City na shirin sayen shahararren dan wasan gaban nan mai suna Luis Hernandez mai shekaru ashirin da bakwai da haihuwa.

Ita kuma kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta shirya tsaf domin sayen dan wasan kungiyar Schalke 04 mai suna Leroy Sane dan shekaru ashirin da haihuwa a kan kudi fan miliyan arba’in.

Idan muka koma kungiyar kwallon kafa ta Juventus dake kasar Germany kuma, ta ce bata da masaniyar wata kungiyar kwallon kafa da take zawarcin dan wasanta mai suna Paul Pogba mai shekaru ashirin da uku da haihuwa.

Shi kuma Zlatan Ibrahimovic ya bayyana wa jama’a sanarawar cewa zai ajiye takalmansa na taka leda da yake yiwa kasar sa wato Sweden bayan an kammala wasannin cin kofin nahiyar Turai da ake bugawa a Faransa.

Saurari Rahoton A Nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:05 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG