Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dr. Fahad Dan Najeriya Mai Bincike Akan Kula Da Lafiyar Jama'a


Dr. Fahad Galadanci
Dr. Fahad Galadanci

Fahad Mukhtar Galadanci likita ne daga karamar hukumar Gwale dake jihar kano, Najeriya. Wanda yanzu haka yana kokarin kamala karatun shi na Digirin digirgir “Ph.D” a jami’ar South Florida a garin Tampa, jihar Florida dake Amurka.

Fahad ya bayyana yadda ya fara samun sha’awar karatun likitanci tun a kuruciyara shi, kuma ya dau wannan niyya tun a lokacin da yake makarantar sakandare. Ya dukufa da karatu da mai da hankali har zuwa lokacin da Allah, ya bashi nasaran samun shiga jami’ar Bayero University dake Kano. In da yayi karatun zama likita. Duk dai da cewar karatun likitanci nada wahala matuka amma wannan bai hana shi samun kammalawa ba, a shekara ta 2011. Ya kuma yi aiki a asibitin koyarwa na Murtala Muhammad Specialist Hospital a jihar kano bayan lokacin da ya kammala Karatun shin a zama kwararren likita.

A lokacin karatun shi, ya samu sha’awar karo karatu a kasar Waje saboda yana niyyar yin bincike akan lafiyyar da ta shafi Al'umma da yawa, wato “Public Health” akan hakane ya samu takardar karo karatu a Jami’ar Texas A and M dake Amerika. Yana daya daga cikin dalibai 17 da Gwamnatin Jihar Kano ta biya musu dan su karo karatun digiri na biyu “Masters” a shekara ta 2013 a nan kasar Amerika.

Fahad dai ya samu kyakyawan sakamako a karatun shi na “Masters” a jihar Texas ta nan Amurka, wanda hakan ya sa Jami’ar South Florida ta Amurka taga ya cancanta ya karasa karatun shi na Digirin digirgir a wannan fanin wanda ita jami’ar ta dauki nauyin biyya mishi kudin makaranta da kuma bashi aiki a matsayin Mataimakin mai bincike a bangaren lafiya na Alumma.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG