Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Satar Fasaha Babban Kalubale Ga Kannywood


Aisha Amat
Aisha Amat

A filin nishadi yau wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir ta karbi bakunci Aisha Amat mai shirya fina-finai koda yake Aisha bata tsaya akan shirya fina finai kawai ba ta hada har da kasuwanci fina finan.
Ta shafe shekaru 12 tana harkar ta ce abinda ke ciwa masana'antar tuwo a kwarya shine yadda masu satar fasaha ke bata masu kasuwanci su domin da zarar fim ya fito suke satar su kuma yi kwafi da dama wanda kan jawo nakasu ga wadanda suka yi dawainiyar fin din.
Ta ce babban kalubalensu shine duk da kasancewar hukuma na sane da kalubalen da suke fuskanta har kawo yanzu an kasa sawo kan matsalar

XS
SM
MD
LG