Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Emmanuel Amuneke Likkafa Tayi Gaba


Emmanuel Amuneke, wanda ya horas da ‘yan kungiyar wasan kwallon kafa ‘yan kasa da shekaru 17, wato Golden Eagles, likkafa ta yi gaba yanzu shi aka dorawa alhakin horas da ‘yan kungiyar Flying Eagles.

Hukumar wasan kwallon kafa ta Najeriya, wato NFF, ne ta bayana haka a wata sanarwar bayan taron da ta gudanar ranar talatar da ta gabata.

Amma sanarwar ba tace komai akan Manu Garba , wanda Amuneke zai karbi aiki daga hannunsa ba.

Amuneke shi ya kai ‘yan kungiyar Golden Eaglets, ga nasarar lashe kofin kwallon kafa na duniya a shekarar data gabata a kasar Chile.

A zamanin sa Amuneke, ya taba lashe gambin dan wasan da yafi kowa taka leda a Nahiyar Afirka a shekarar 1994, ana kuma sa ran cewa zai kai kungiyar ta Flying Eagles, ga nasarar samun gurbi a gasar cin kofin nahiyar Afirka wanda za’a gudanar a Zambia a shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG